Yara da dama sun kamu da kyanda a Najeriya

Yaro mai fama da cutar gyanda
Image caption Ana alakanta barkewar wannan cuta da yanayin zafi da kuma karancin allura rigakafi

Rahotanni daga Jihohin Katsina da Kano na cewa dubban yara ne suka kamu da cuyar kyanda .

A Katsina an ce cutar ta watsu a dukkan kananan hukumomi 34.

Can ma a Kano hukumomi sun ce yara sama da dubu daya ne suka kamu da cutar ta kyanda, suna kuma jinya a asibitoci daban-daban na jihar.

Kwamishinan lafiya na jihar Dr. Abubakar Labaran yusuf ne ya tabbatar wa BBC hakan.

Masana al'amuran lafiya a Nigeria sun ce a yanzu haka ana fama da annobar kyanda a wasu sassan kasar.

Sai dai wasu rahotannin na cewa an samu karancin allurar rigakafin cutar, abin da ya taimaka wajen barkewarta.

Cutar ta barke ne a wasu kananan hukumomi biyar da suka hada da Tarauni da Gwale da Madobbi da Karaye da kuma Kabo.

A yakin na arewacin Najeriya, har yanzu ana samun iyayen da ba sa bari a yi wa 'ya'yansu alluran rigakafi.