An fara kirga kuri'u a zaben Kenya

Image caption Tun da karfe shida ne agogon Kenya, mutane da dama suka fito domin kada kuri'a

An fara kirga kuri'u a zaben kasar Kenya wanda masu sa ido suka ce shi ne mafi muhimmancin a tarihin kasar.

Kamata yayi a rufe mazabun kada kuri'a da misalin karfe 2:00 agogon GMT, sai dai jami'ai sun ce za a bar wadanda ke kan layi su kada kuri'unsu.

Tun da farko an samu tashin hankali a garin Mombasa mai tashar jiragen ruwa, inda aka kashe 'yan sanda biyar a hari guda.

Sakamakon farko ya nuna cewa manyan 'yan takarar shugabancin kasar biyu sun yiwa ragowar fintinkau.

Kuri'un da aka fara kirgawa daga mazabun da aka kammala akan lokaci, sun nuna Uhuru Kenyatta na gaban Fira Minista Raila Odinga.

Sai dai masu lura da al'amura sun ce sakamakon ba zai yi wani tasiri ba kawo yanzu ganin cewa ya fito ne daga yankunan da Mr Kenyatta ke da karfi.

Wannan ne karon farko da ake gudanar da zabe a karkashin sabon tsarin mulkin kasar, wanda aka tsara domin kaucewa maimaita rikicin da ya biyo bayan zaben shekara ta 2007.

An kara lokacin zaben

Mataimakiyar shugaban hukumar zabe a kasar Kenya Lilian Mahiri Zaja ta ce ana kada kuria kamar yadda sabon kundin tsarin mulkin kasar ya tanada kuma komai na tafiya daidai.

Sai dai ta amince cewa an fusknaci matsaloli kan tsarin da aka fitar domin rage zamba a lokutan zabe.

Ta kuma ce rumfunan zabe za su kasance a bude har zuwa karfe goma sha biyu na tsakar dare domin ba kowa damar kada kuri'a.

Sama da mutane 1,000 ne da ba basa ga maciji da juna suka rasa rayukansu, bayan rikicin da ya barke a wancan lokacin.

Duk da cewa dai an yi gangamin neman zaman lafiya, rahotanni sun ce an kashe jami'an 'yan sanda biyu a kusa da Mombasa da safiyar ranar Litinin.

Jami'ai sun ce wasu gungun mutane ne suka kaiwa 'yan sandan hari, a yankin Changamwe a bayan garin Mombasa.

Al'ummar Kenya na zabar 'yan majalisa da gwamnonin lardi da kuma yan majalisun lardi.

Sai dai duniya ta sanya ido ne a kan zaben shugaban kasa.

'Yan takara takwas ne ke neman kujerar shugaban kasa, amma yan takarar dake gaba-gaba sune fira minista mai ci a yanzu, Raila Odinga da kuma Uhuru Kenyatta.

Karin bayani