Jama'ar Kenya na kada kuri'a

Image caption Tun da karfe shida ne agogon Kenya, mutane da dama suka fito domin kada kuri'a

Jama'ar kasar Kenya na kada kuri'a a zaben da masu sanya ido suka bayyana da cewa shi ne mafi mahimmanci a tarihin kasar.

Wannan ne karon farko da ake gudanar da zabe a karkashin sabon tsarin mulkin kasar, wanda aka tsara domin kaucewa maimaita rikicin da ya biyo bayan zaben shekara ta 2007.

Sama da mutane 1,000 ne da ba basa ga maciji da juna suka rasa rayukansu, bayan rikicin da ya barke a wancan lokacin.

Duk da cewa dai an yi gangamin neman zaman lafiya, rahotanni sun ce an kashe jami'an 'yan sanda biyu a kusa da Mombasa da safiyar ranar Litinin.

Akalla mutane shida - ciki harda maharan - aka bada rahoton sun mutu a harin na Changamwe, mai nisan sa'a guda daga tsakiyar garin Mombasa.

Jami'ai sun ce wasu gungun mutane ne suka kaiwa 'yan sandan hari, a yankin Changamwe a bayan garin Mombasa.

Al'ummar Kenya za su zabi, 'yan majalisa da gwamnonin lardi da kuma yan majalisun lardi.

Sai dai duniya ta sanyan ido ne a kan zaben shugaban kasa.

'Yan takara takwas ne ke neman kujerar shugaban kasa, amma yan takarar dake gaba-gaba sune fira minista mai ci a yanzu, Raila Odinga da kuma Uhuru Kenyatta.

Karin bayani