Dogayen layuka a zaben kasar Kenya

Image caption Tun da karfe shida ne agogon Kenya, mutane da dama suka fito domin kada kuri'a

An bayar da rahotannin dogayen layuka a sassan kasar Kenya da dama inda jama'a suka fita domin kada kuri'a a zaben kasa baki daya tun bayan zaben shekara ta 2007 wanda ya haifar da mummunan tashin hankali.

Jama'a sun yi korafin cewa suna shafe dogon lokaci a cikin zafin rana kafin su kada kuri'a.

An samu rahotannin tashin hankali a garin Mombasa mai tashar jiragen ruwa inda aka kashe akalla 'yan sanda biyar.

Wannan ne karon farko da ake gudanar da zabe a karkashin sabon tsarin mulkin kasar, wanda aka tsara domin kaucewa maimaita rikicin da ya biyo bayan zaben shekara ta 2007.

An kara lokacin zaben

Mataimakiyar shugaban hukumar zabe a kasar Kenya Lilian Mahiri Zaja ta ce ana kada kuria kamar yadda sabon kundin tsarin mulkin kasar ya tanada kuma komai na tafiya daidai.

Sai dai ta amince cewa an fusknaci matsaloli kan tsarin da aka fitar domin rage zamba a lokutan zabe.

Ta kuma ce rumfuna zabe za su kasance a bude har zuwa karfe goma sha biyu na tsakar dare domin ba kowa damar kada kuri'a.

Sama da mutane 1,000 ne da ba basa ga maciji da juna suka rasa rayukansu, bayan rikicin da ya barke a wancan lokacin.

Duk da cewa dai an yi gangamin neman zaman lafiya, rahotanni sun ce an kashe jami'an 'yan sanda biyu a kusa da Mombasa da safiyar ranar Litinin.

Jami'ai sun ce wasu gungun mutane ne suka kaiwa 'yan sandan hari, a yankin Changamwe a bayan garin Mombasa.

Al'ummar Kenya za su zabi, 'yan majalisa da gwamnonin lardi da kuma yan majalisun lardi.

Sai dai duniya ta sanyan ido ne a kan zaben shugaban kasa.

'Yan takara takwas ne ke neman kujerar shugaban kasa, amma yan takarar dake gaba-gaba sune fira minista mai ci a yanzu, Raila Odinga da kuma Uhuru Kenyatta.

Karin bayani