An kashe sojojin Syria 40 a Iraki

Taswirar Iraki

Akalla sojojin kasar Syria 40 ne da wasu ma'aikatan gwamnati aka kashe a gundumar Anbar da ke yammacin kasar Iraki, a cewar jami'ai a birnin Bagadaza.

Suna cikin wasu gungun jama'a da suka tsallaka cikin Irakin daga Syria domin kaucewa hare-haren dakarun da ke adawa da gwamnati, a cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Ana tafiya da su kan iyaka ne lokacin da wasu 'yan bindiga da ba a fayyace ba suka bude musu wuta. Akwai 'yan kasar ta Iraki ma a cikin wadanda suka mutu.

Shekara biyu kenan aka shafe ana rikici a kasar ta Syria.

Dubun dubatar jama'a ne suka rasa rayukansu sakamakon fadan da ake gwabzawa tsakanin dakarun shugaba Bashar al-Assad da masu adawa da shi.

Rukunin sojin na Syria sun shiga Iraki ne ta kan iyakar Yaarubiyeh a karshen mako, bayan da dakarun gwamnati suka kaddamar da hare-hare a yankin, kamar yadda wani babban jami'in Iraki ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Ya kara da cewa: "yan bindiga sun yi musu kwantan bauna sannan suka kashe 40 daga cikinsu, tare da wasu sojojin Iraki da ke basu kariya."

Karin bayani