HIV: An warkar da wata karamar yarinya a Amurka

Image caption Kwayar cutar HIV

Wasu masana a Amurka a karon farko sun warkar da wata karamar yarinya da aka haifa da kwayar cutar HIV mai karya garkuwar jiki a jihar Mississippi.

Dr Deborah Persaud, mai nazarin kwayar cututuka ce ta asibitin Jam'iyyar Baltimore ta bayana irin nasarar da suka samu a wani babban taron nazarin manyan cututuka da aka gudanar a Atlanta.

A yanzu haka dai yarinyar tana da shekaru biyu da rabi da haihuwa kuma ta kwashe kimanin shekara daya ba ta sha magani ba.

An dai gwada ta kuma babu alamar cutar ko kadan a jikinta.

Masanan dai sun ce za su ci gaba da gwadata domin su tabbatar cewa irin maganin da aka yi mata zai iya yiwa sauran yara aiki.

Masu nazarin suna ganin sun samu nasara ne saboda sun tukarin cutar da wurin tun kafin ta samu inda za ta boye.

Dr Deborah Persaud ta ce idan har cutar ta samu makwanci ne a cikin jiki ta ke ginuwa har ta zuwa cutar AIDS.

Amma suna ganin wannan nasara da suka yi a kan yarinyar zai taimaka wajen samar da magani ga yara masu dauke da kwayar cutar ta HIV.

Idan har an tabbatar da lafiyar yarinyar, za ta zama mutun na biyu a duniya da aka samu cewa sun warke daga kwayar cutar.

Timothy Ray Brown ne ya zama mutun na farko da aka warkar da ga cutar ta HIV a shekara ta 2007.