Birnin fasahar kere-kere a Ghana

Ana  bajekolin fasahar kere-kere na duniya a kowace shekara
Image caption Ana bajekolin fasahar kere-kere na duniya a kowace shekara

A Ghana an kaddamar da aikin wani katafaren gini, da zai samar da ayyukan yi ga masu fasahar kere-kere.

An bayyana cewa ginin, wanda aka sanya wa suna Birnin Muna Fata, wato Hope City a turance, zai kunshi cibiyar harhada kayayyakin lantarki da na lataroni mafi girma a duniya.

Haka kuma birnin da za a shimfida, zai kunshi gini mafi tsawo a nahiyar Afirka.

Shugaban kasar, John Dramani Mahama ne ya kaddamar da ginin, kuma bikin kaddamarwar ya samu halartar wasu gwamnoni biyu daga Najeriya da wani babban jami'i na kamfanin Microsoft.

Wasu kamfanoni masu zaman kansu ne suka kuduri aniyar aiwatar da birnin, a karkashin jagorancin wani babban kamfanin kere-kere a Ghana mai suna ROG da cikkakken goyon bayan gwamnatin kasar.

Idan aka kammala ginin birnin, ana fatan mutum dubu hamsin za su samu aikin yi.

Za a kashe dala biliyan goma wajen gina Birnin Muna Fatan, kuma za a kammala shi nan da shekaru hudu masu zuwa.