An fara samun sakamako a Kenya

Jama'ar kasar Kenya na jiran sakamakon zaben shugaban kasa bayan da miliyoyin mutane suka kada kuri'unsu a ranar Litinin.

Bayan da aka kirga daya bisa uku na kuri'un da aka kada a zaben shugaban kasa, mataimakin Fira Minista Uhuru Kenyatta na gaban babban abokin takararsa Fira Minista Raila Odinga.

Shugaban Hukumar Zaben na Kenya, Ahmed Issack Hassan ya ce sakamakon da ke fitowa a yanzu haka na wucin gadi ne kuma ya bukaci al'ummar kasar da su yi hakurin jiran cikakken sakamakon zaben.

Ya ce sama da kashi saba'in ne cikin dari na masu zabe su ka fito kada kuri'a.

Mr Hassan ya yabawa masu kada kuri'a saboda irin da'ar da su ka nuna a lokacin gudanar da zaben.

Laifukan yaki

Amma masu sa'ido na cewa wadannan sakamakon na wucin gadi dake fitowa an samu su ne daga garuruwan da Mr. Kenyatta ke tasiri.

Mr Kenyatta zai bayyana a gaban kotun hukunta manya laifukka dake Hague domin amsa tuhumar da ake masa na cewa yana da hannu a tashin hankalin da ya auku bayan zaben da aka gudanar a shekara ta 2007, zargin da kuma ya musanta.

Jami'an hukumar zabe sun ce adadin mutanen da suka fito a bana sun haura wadanda su ka fito a zaben da aka gudanar a shekara ta 2007.

Masu sa'ido dai sun nuna damuwa kan yiwuwar barkewar tashin hankali muddin daya daga cikin manyan 'yan takara biyu bai samu sama da kashin hamsin na kuri'un da aka kada ba.

Mahukunta dai sun gargadi al'ummar Kenya da kada su bari a samu tashin hankali kamar irin wanda ya auku a shekara ta 2007 wanda ya yi sanadiyar mutuwar sama da mutane dubu daya bayan anyi zargin magudi a zaben.

Karin bayani