An ci tarar kamfanin Microsoft a Turai

microsoft
Image caption Microsoft na daya daga cikin manyan kamfanoni a duniya

Hukumar Tarayyar Turai ta ci kamfanin samar da manhaja na Amurka wato Microsoft tarar dala miliyan 750 da akan saba alkawarin da ya yi na baiwa abokan huldarsa zabin manhajar shiga internet.

Wannan dai ita ce tara mafi girma da Tarayyar Turan ta taba sawa kan irin wannan laifi.

Kamfanin Microsoft din ya amsa kuskuransa.

Microsoft ya karya yarjejeniyar da ya kulla da masu sa ido kan samar da manhaja na Turai a shekara ta 2009.