Ana zaman makokin Chavez a Venezuela

Shugab Hugo Chavez
Image caption Marigayi Hugo Chavez ya rasu ne yana shekara 58 a duniya

An bayyana zaman makoki na kwanaki bakwai a kasar Venezuela domin girmama Hugo Chavez, wanda ya mutu a matsayin shugaban kasar yana da shekaru 58.

Dubban magaoya bayansa ne suka fito kan tituna domin juyayin mutuwar shugaban.

Sun taru a kan tituna a lokacin da ake wucewa da gawar Mr Chavez wacce aka dauka domin kaita makarantar sojoji inda za a binne shi ranar Juma'a.

Mr Chavez wanda ya yi kaurin suna wurin sukar Amurka, ya shafe fiye da shekara guda yana fama da kazamar cutar Daji.

An yi kasa-kasa da tutar kasar domin girmama shugaba Chavez.

Nan da kwanaki 30 ne za a sanar da lokacin da za a gudanar da zaben sabon shugaba a kasar- kafin sannan, mataimakin shugaban kasa Nicolas Maduro ne zai jagoranci kasar kafin a gudanar da zabe.

Sakonnin ta'aziyya

Shugabannin kasashen Latin Amurka sun fara isa Caracas babban birnin kasar domin girmamawa - daga cikinsu akwai shugaba Cristina Fernandez ta Argentina, Jose Mujica na Uruguay da Evo Morales na Bolivia.

Kasar Ecuador ta bayyana kwanaki uku na zaman makoki, yayin da shugaban Iran Mahmoud Ahmadinejad, ya bayyana makokin kwana guda a kasarsa sannan ya bayyana shi a matsayin wanda "ya sadaukar da ransa".

Shugaba Obama wanda suka samu sa'insa da Hugo Chavez a lokacin da yake raye ya ce Venezuela na fuskantar kalubale sakamakon mutuwar shugaban nata, sanna ya ce kasar Amurka na sake jaddada cewa shirye take da ta ci gaba da taimakawa al'ummar kasar.

Shima jakadan Rasha a majalisar dinkin duniya cewa ya yi;

"abin tashin hankali ne, Mr Chavez wani gwarzon dan siyasa ne ga kasarsa,da yankin latin amurka kai harma da duniya baki daya daya."

Shugabar kasar Argentine Cristian Fernandes ta ce ta soke duk wasu abubuwa da za ta yi a lokacin da ta samu labarin rasuwar abokinta kuma ta ayyana kwanaki uku da za a yi jimami a kasarta.

Shi ma Tsohon Shugaban kasar Cuba Fidel Castro ya yi jimamin rasuwar mutumin da yake tamkar da a gare shi kuma kasar Cuba ta ce ranar da za a yi jana'izar Chavez rana ce ta hutu ga al'ummar kasar.

Karin bayani