Shugaba Goodluck zai kai ziyara Borno da Yobe

Image caption Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan

A Najeriya, a yau ne shugaban kasar Dr Goodluck Jonathan zai fara wata ziyarar aiki a jihohin Borno da Yobe.

Yankin da jihohin su ke sun yi fama da hare-haren kungiyar Jama'atu Ahlissunnah Lidda'awati wal Jihad da wasu ke kira Boko Haram.

Shugaban kasar dai zai kai ziyarar ne bayan wata ziyarar da gwamnoni goma na sabuwar jam'iyyar adawa ta APC suka kai yankin.

Sai dai masu nazarin alamurra na ganin ziyarar Shugaban kasar ta zo a makare.

Dr. Abubakar Kari na Jami'ar Abuja ya ce yana ganin Shugaban kasar zai ziyarce saboda manufar siyasa.

Masu magana da yawun gwamnati sun musanta haka inda su ka ce shugaban kasar ya damu da yankin matukka kuma a kullum ya lallubo hanyoyin magance matsalar da ya ke addabar yankin.