Jonathan ya nemi Boko Haram su bayyana kansu

Goodluck Jonathan
Image caption Wannan ne karon farko da shugaban ya ziyarci jihohin a cikin shekaru uku na mulkin kasar

Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya ya ce ba zai shiga tattaunawa kan batun ba da afuwa ga 'yan kungiyar da aka fi sani da Boko Haram ba, sai fa idan sun fito sun nuna kansu.

Shugaba Jonathan ya bayyana haka ne a Damaturu, babban birnin jihar Yobe, a ziyarar yini biyu da ya fara yau a jihohin Borno da Yobe.

A lokacin ziyarar tasa a Damaturu a yau da rana, Shugaba Jonathan ya gana da dattawa da shugabanin Jihar, inda su ka tattauna akan matsaloli da ke addabar jihar da kuma hanyoyin da za a bi domin samun zaman lafiya.

Alhaji Adamu Chiroma, tsohon ministan kudi a Nigeria na daga cikin dattawan da su ka gana da Shugaban ya kuma sake nanata kiran da Sarkin Musulmi ya yi na cewa gwamnati tai wa 'yan Kungiyar Boko Haram afuwa, yana mai cewa 'muna sake nanata wannan kira'.

'Akwai hankali da hikima a cikin wannan hanya na bada afuwa, sannan kuma a tattauna da su' in ji Malam Adamu Chiroma.

Karin bayani