Shugaba Jonathan na ziyara a Yobe da Borno

Goodluck Jonathan
Image caption Wannan ne karon farko da shugaban ya ziyarci jihohin a cikin shekaru uku na mulkin kasar

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya isa birnin Damaturu, a ziyar aikin da yake yi a jihohin Borno da Yobe, wadanda ke fama da hare-haren kungiyar Boko Haram.

Ziyarar tasa ita ce ta farko tun bayan da ya hau kujerar mulkin Najeriya a shekarar 2010, kuma ita ce ta farko tun bayan fara tashin hankalin da jihohin ke fuskanta daga Boko Haram shekaru uku da suka wuce.

Bayan ya sauka a jirgi a Maiduguri na jihar Borno, shugaban Najeriyar ya shiga wani karamin jirgin sama zuwa Damaturu babban birnin jihar Yobe.

Bayanai sun nuna cewa abubuwan da shugaban zai yi a ziyarar sa ta jihar Yobe, sun hadar da gana wa da sarakunan gargajiya da sauran jama'a a gidan gwamnan jihar Yoben.

Mr. Jonathan zai kuma kadamar da wasu ayyukan ci gaba da gwamnatin jihar Yoben ta gudanar.

Ana sa ran shugaban kasar da tawagar sa za su koma jihar Borno da yammacin Alhamis, inda zai kwana a Maiduguri, kuma a can ma zai kadamar da wasu ayyukan, ya kuma yi taro da jama'a kafin ya yi bankwana da yankin.

Jihar Yobe dai ta baiwa ma'aikata hutu ranar Alhamis yayin da jihar Borno ta sanar da ranar Juma'a a matsayin hutu.

Wasu mazauna Damaturu da Maiduguri sun bayyana damuwarsu bisa takaita zirga-zirga da aka yi, a yankunan da shugaban kasar ke ziyara.