Harkar kiwo lafiya ya tabarbare a Syria

Image caption Harkar kiwon lafiya na fuskantar koma baya a Syria

Kungiyar likitoci ta Medecins Sans Frontieres ta nuna damuwa matuka game da yadda harkar kiwon lafiya ya tabarbare a kasar Syria.

Hakan na nuna cewa marasa lafiya da wadanda suka samu rauni na cikin hadari sakamakon durkushewar kiwon lafiya a kasar.

Kungiyar ta MSF ta ce a baya dai harkar kiwon lafiyan syria na da matukar inganci, amma tunda aka fara rikicin kasar ake wa likitoci kallon makiyan kasar.

Gwamnatin kasar tana zargin likitoci da kula da 'yan tawayen da su ka yi rauni.

Kungiyar ta ce hare-haren da gwamnati ke kaiwa ta sama ya sanya asibiti na uku dakatar da aiki,

Asibitocin wucin gadi ma na fuskantar barazanar kai hare-hare.

Ya yin da ake karancin magungunana a yankunan gwannati da na 'yan tawayen ana kuma bada fifiko wajen samar da magunguna ga mayaka akan fararen hula.

Karin bayani