An amince John Brennan ya jagoranci CIA

Image caption Barack Obama Shugaban Amurka ya amince da nadin John Brennan a matsayin sabon Daraktan CIA

Majalisar Dattawa a birnin Washington ta Amurka ta tabbatar da nadin John Brennan a matsayin sabon Darakta na kungiyar leken asiri ta kasar wato CIA.

Mr Brennan wanda shine babban mai bawa Shugaba Obama shawara kan harkokin yaki da ta'addanci a can baya ya yi aiki na tsawon shekaru ashirin da biyar da kungiyar ta CIA.

Wani Sanata ne na jam'iyyar Republican ya jinkirta tabbatar da shi kan mukamin, saboda sa'oi kimanin goma sha-ukku da ya shafe yana neman karin bayani a kan manufar gwamnatin Amurka ta harin da ta ke kaiwa da jiragen sama wadanda babu matuka a cikin su.

Karin bayani