Mahakar Uranium ta Imuraren za ta soma aiki a 2015

Mahamadou Issoufou
Image caption Za a soma hakar Uranium a Nijar daga 2015

A Jamhuriyar Nijar kamfanin AREVA mai hakar Uranium a kasar ya ce a tsakiyar shekara ta 2015 ne zai fara aikin hakar uranium din yankin Imuraren.

Mataimakin Darekta Janar na kamfanin na AREVA Mista Olivier Wantz ne ya tabbatar da haka jiya a birnin Yamai.

Yankin na Imuraren dai na iya samar da tan dubu biyar kowacce shekara har tsawon shekaru arba'in

Idan aka soma aikin, Nijar za ta kasance kasa ta farko mai arzikin Uranium a nahiyar Afirka.

Karin bayani