China ta yi gargadi kan yankin Koriya

Image caption Shugaban Koriya ta Arewa ya kai ziyara iyakar su da Koriya ta Kudu

Kasar China ta nemi kasashen Koriya da abokan huldarsu da su kwantar da hankali, bayan da Koriya Korea ta Arewa ta ce za ta kawo karshen duk wata yarjejeniyar zaman lafiya da Korea ta Kudu.

Koriya ta Arewa ta sanar da cewa za ta kawo karshen duk wata yarjejeniyar zaman lafiya da Koriya ta Kudu don mayar da martani ga wani sabon jerin takunkumin da Majalisar Dinkin Duniya ta garkamawa Koriyar ta arewa bayan ta yi gwajin makamin nukiliya na uku.

A wata sanarwa da ta bayar 'yan sa'oi bayan an amince da matakan na Majalisar Dinkin Duniya, Koriya ta Arewar ta ce za ta rufe babbar kan iyakar da ta hada kasashen biyu dake Pan-Munjom, za ta kuma tsinke muhimmiyar hanyar sadarwar da ta hada Arewacin da Kudancin.

Wakiliyar BBC a birnin Seoul ta ce yawancin 'yan Koriyar ta Kudu ba sa tunanin Koriyar ta Arewa za ta aiwatar da barazanar kaddamar da harin nukiliya na ba-zata a kansu.

Sai dai ta ce suna da wannan fargabar yanzu fiye da rikice-rikicen da suka faru a can baya.

Karin bayani