Venezuela ta dage ranar Jana'izar Chavez

Image caption 'Yan Venezuela na alhinin mutuwar Hugo Chavez

Gwamnatin Venezuela ta sanar da cewa za ta ajiye gawar marigayi Shugaba Hugo Chaves a wani wuri na musamman har zuwa a kalla wasu kwanaki bakwai masu zuwa don bai wa magoya bayansa damar yi masa bankwana na karshe.

Mataimakin Shugaban kasar Nicolas Maduro ya ce za a yi wa gawar ta Hugo Chaves tambari daga bisani a sanya ta a cikin wani akwatin gawa na gilas a wani wurin ajiye kayan tarihi.

Ya ce, "gwamnati ta yanke shawarar kara tsawon lokacin da za a ajiye gawar ne saboda ganin irin yadda 'yan kasar ta Venezuela fiye da miliyan biyu suka shafe sa'oi da dama a layi domin wucewa gaban akwatin gawar ta Mr Chaves su yi masa addu'ar ban girma."

Karin bayani