'Yan Venezuela na taron makokin Chavez

Makokin Shugaba Chavez
Image caption Za a ajjiye gawar Chavez a gidan tarihi

Dubun dubatan jama'a sun yi ta tururruwa tun da sanyin safiya a Caracas babban birnin kasar Venezuela domin jana'izar marigayi shugaba Hugo Chavez.

Za'a ci gaba da ajiye gawarsa na karin wasu kwanaki bakwai domin baiwa jama'a damar yi masa kallo na karshe da ban kwana.

Gwamnatin ta sanar da cewa gawar Mr Chavez wadda aka alkinta ta da sinadaran kimiyya za'a ajiye ta dundundun a gidan tarihi na soji.

Mataimain Shugaban kasar Nicolas Maduro yace za'a adana da kuma karrama gawar Chavez ce kamar yadda aka yiwa sauran yan gwagwarmayar juyin-juya hali a fadi duniya.

Karin bayani