'Yan sandan da ake zargin kisan dan Taxi na kotu

Image caption Dan Taxin da ake zargin 'yan sandan Afrika ta Kudu da kashewa

A kasar Afrika ta kudu wasu 'yan sandan kasar su 9 sun gurfana gaban Kotu inda aka yi zaman sauraren kara ta neman belinsu dangane da mutuwar wani direban Taxi dan kasar Mozambique.

An sanya wa Mido Macia ne ankwa aka daure shi jikin motar 'yan sanda aka rinka jan sa a kan titunan Daveyton dake kusa da Johannesburg.

Dukkan 'yan sandan 9 dai sun ce ba su da laifi ga cajin da aka yi musu na kisan kai.

Hoton video na abinda ya faru da wasu suka dauka da wayar salula wanda aka nuna a gidan talabijin na kasar ya tunzura mutane a sassa daban-daban na kasar.

Karin bayani