An bawa Malamai bindiga a Amurka

Image caption South Dakota inda aka amincewa Malamai kare kansu da bindiga

Jihar South Dakota dake kasar Amurka ta zartar da wata doka wadda ta amince wa makarantun yankin baiwa Malaman makaranta da sauran ma'aikatan makarantun bindigogi don su rinka bayar da kariya ga dalibansu.

Ita ce Jiha ta farko da ta amince da haka tun bayan wani kisan gilla da aka yi a Newtown cikin watan Disambar bara inda aka kashe yaran makarantar ashirin da malamai shida.

Uta da wasu larduna a Texas dama sun rigaya sun amince wa malamai su rika rike bindigogi.

Gwamnan jihar South Dakota Dennis Daugaard ya ce a Jihohi na karkara kamar na su, ba kasafai a kan samu jami'an tsaro a kusa ba.

Karin bayani