Jami'an Diplomasiyya na binciken kisan 'yan kasashen waje

Jami'an Diplomasiyya na bincike kan kisan da wata Kungiya ta ce tayi wa wasu yan kasashen waje su bakwai wadanda aka yi garkuwa da su.

Wata ƙungiyar masu gwagwarmaya da makamai a arewacin Najeriya mai suna Ansarul muslimina fi biladi sudan tace ta kashe 'yan ƙasashen waje bakwai da ta sace a watan da ya gabata.

Ƙungiyar ta Ansaru tace ta ɗauki wannan matakin ne saboda dakarun Najeriya da na Faransan sun kashe musulmi a wani farmakin da suka kai na ƙoƙarin su na 'yanto waɗanda aka yi garkuwar da su.

Mutanen da aka yi garkuwar da su dai ma'aikata ne na wani kamfanin gine gine mallakar 'yan Lebanon

Uku daga cikin mutanen dai 'yan Labanon ne, sauran hudun kuwa sun fito ne daga ƙasashen Burtaniya, da Girka, da Italiya, da kuma Philippines.

Ana dai tunanin cewa ƙungiyar ta Ansaru, ɓangare ne na ƙungiyar Boko Haram wacce aka yi imanin cewar ita ke riƙe da iyalan Faransawan nan da aka sace a Kamaru.