A gaggauta zabe a Venezuela–Maduro

Image caption Shugaba Nicolas Maduro ya ce a gaggauta zabe a Venezuela

Shugaban kasa na riko a Venezuela Nicolas Maduro ya umarci hukumomin zaben kasar su gaggauta shirya zaben Shugaban kasa.

An rantsar da Mr Maduro a wani biki da aka yi a majalisar dokokin kasar kwanaki uku bayan mutuwar Shugaba Hugo Chavez.

A jawabin da ya shafe sa'a daya yana yi, ya yi alkwarin cigaba da aiwatar da manufofin magabacinsa.

Mr Maduro ya ce, "muna godiya a gare ka, akwai wani sabon shiri da muke da shi, kuma wannan ne za mu yi wa kan mu."

Yawancin 'yan majalisar 'yan adawa ba su halarci bikin rantsuwar ba, suna cewa a karkashin tsarin mulki, Shugaban majalisar dokokin kasar ne ya kamata ya karbi ragamar Shugabancin kasar.

Jagoran 'yan adawar Henrique Capriles, ya ce 'yan kasar Venezuela ba su zabi Mr Maduro ba.

Karin bayani