Masu zanga-zanga sun fantsama a Masar

Image caption Masu zanga zanga sun fantsama a kan titunan Masar

Masu zanga-zanga sun fantsama a kan tituna a kasar Masar sakamakon wani hukuncin kotu game da tarzomar da aka yi a lokacin gasar kwallon kafa tsakanin wasu kungiyoyin kwallon kafar Port Said da Alkahira a bara; inda aka kashe fiye da mutane 70.

Kotun ta tabbatar da hukuncin kisan da aka yanke wa mutane 21 magoya bayan al-Masry daga Port Said abinda ya haddasa zanga-zanga a birnin.

Sai dai kuma Kotun ta wanke karin wasu mutanen 28 dake kare kansu - wadanda suka hada da 'yansanda bakwai - abinda ya haddasa rikicin a birnin Alkahira a tsakanin magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta al-Ahly wadda magoya bayan ta ne mafi rinjayen wadanda aka kashe a tarzomar ta asali.

Ahmed Rashway wani lauya a Alkahira ya ce shi ya gamsu da hukuncin Kotun.

Yace,"Ina ganin hukuncin Kotun a kan yawancin wadanda ta tuhuma abin amincewa."

Karin bayani