Japan: anyi zanga-zangar adawa da nukiliya

Image caption Masu zanga-zangar adawa da makamashi nukiliya

Dubun dubatar masu zanga zangar ƙin jinin nukiliya sun gudanar da wani gangami a birnin Tokyo a ranar jajiberin cika shekaru biyu da bala'in tsahar nukiliya ta Fukushima.

Masu zanga zangar sun yi ƙira ga gwamnatin Japan data yi watsi da dukkanin makamashin nukiliya

Wasu dai sun bayyana damuwa game da shirye shiryen da sabuwar zaɓaɓɓiyar gwamnatin ƙasar mai ra'ayin riƙau take yi na sake buɗe wasu tashoshin nukiliyar ƙasar

A yanzu dai guda biyu ne kachal ne suke aiki, bayan an rufe su baki dayan sauran tashoshin sakamakon girgizar kasar data afkawa kasar da bala'in Tsunami wanda ya haddasa wata narkewa a tashar nukiliya ta Fukushima.

Wannan bala'i dai yasa dubun dubatar jama'a a ƙasar tserewa daga gidajensu.