Wanda ake zargi da fyade a India ya kashe kansa –' Inji 'Yansanda

Image caption Tahir gidan yarin da aka sami gawar Ram wanda ake zargi da fyade

Babban wanda ake zargi da yin fyaden taron dangi a birnin Delhi na India an same shi a mace a dakinsa na gidan yari.

Ram Singh, na daya daga cikin samari biyar da ake zargi da fyade da kuma kisan wata yarinya 'yar makaranta a watan Disambar bara.

Lauyan da yake kare babban wanda ake tuhumar da fyaden ya ce 'yan sanda sun kirashi sun shaida masa cewa wanda yake karewa ya kashe kansa.

Ram Singh, shine matukin motar kirar Bus din da aka yiwa 'yar makarantar kazamin fyaden.

Mutuwar Mr Singh za ta jawowa Hukumomi abin fada wanda tuni suna samun matsin lamba kan shari'ar.

Karin bayani