Ana ganawa mutane azaba a Iraqi–Amnesty

Image caption Amnnesty na ikirarin ana ganawa mutanen Iraqi azaba

Bayan kusan kimanin shekaru goma da mamayar da Amurka ta jagoranta a kasar Iraqi kungiyar kare hakkin dan adam Amnesty International ta ce har yanzu ana gana wa mutane azaba a kasar.

Kungiyar ta ce Iraqin tana daga cikin kasashen duniya dake sahun gaba wajen yanke wa mutane hukuncin kisa.

Ta ce ana yanke ma fursunoni da dama hukuncin kisa bayan an yi musu shari'a ta son zuciya.

Amnesty International ta ce an zartas wa mutane 447 hukuncin kisa tun daga shekara ta dubu biyu da biyar lokacinda aka dawo da hukuncin kisa.

Ana kuma tsare da dububban 'yan kasar ta Iraqi ba tare da wata tuhuma ba.

Rahoton na Amnesty ya yi nuni da cewa a yanzu 'yan kasar sun fi samun 'yanci fiye da zamanin mulkin Sadddam Hussain.

Karin bayani