An gayyato Kamfanonin Dubai zuwa Kano

Gwamnan Kano Rabiu Kwankwaso
Image caption An gayyato Kamfanonin Dubai zuwa Kano

Gwamnatin jihar Kano ta ce ta cinma wasu shirye shirye da wasu kamfanoni a Dubai, wadanda za su je Kanon su saka jari a harkar da ta shafi sufurin jirgin kasa da zai rika zirga zirga a cikin birnin Kano.

Baya ga wannan gwamnatin Kanon na tattaunawa da wasu kamfanonin Dubai domin su zuba jari a bangaren hasken wutar lantarki da kuma kafa jami'a mai zaman kanta.

Gwamna Rabi'u Kwankwaso ya shaidawa BBC cewa a watan gobe su ke sa ran daddalewa kan wadannan batutuwan da mutanen da suka gayyata zuwa Kano.

Jahar Kano dai ta yi fama da matsalolin hare haren 'yan bindiga abinda ya kawo cikas ga harkokin kasuwanci

Karin bayani