Koriya ta kudu ta fara atisaye na biyu

Image caption Sojojin Koriya ta kudu na gadi

An fara zagaye na biyu na atisayen shekara-shekara da sojoji kan yi a Korea ta Kudu.

An tara sojoji dubu goma sha-uku 'yan Korea ta Kudun da Amurka.

Dama dai an riga an yi nisa a wani babban atisayen da ake yi a mashigin na Korea.

Korea ta arewa dai ta yi kashedin cewa za ta janye duk wata yarjejeniyar zaman lafiya da ta shafi tsakanin ta da Korea ta Kudu.

Wani wakilin BBC a birnin Seoul ya ce zaman zullumin da ake yi a yankin ya zarce na kowanne lokaci sakamakon gwajin baya-bayan nan na nukiliya.

Karin bayani