Burkutu ta kashe mutane da dama a Libya

Libya
Image caption Daruruwan mutane na kwance a Turabulus

Mutane sama da hamsin ne ake cewa sun mutu daga cikin daruruwa da aka kwantar a asibitoci a duk fadin Turabulus, babban birnin kasar Libya, sakamakon shan gurbatacciyar giyar gargajiya wato burkutu.

Ma'aikatar lafiya ta Libyar ta yi shelar cewa an shiga wani yanayi na ta-baci, a asibitocin kasar.

Tun daga ranar Asabar aka fara samun mace macen, kuma adadin ya ci gaba da karuwa.

Karin bayani