Za a fafata tsakanin Maduro da Capriles a Venezuela

Image caption henrique Capriles jagoran adawa a Venezuela za su fafata da Nicolas Maduro

Yayinda magoya bayan Hugo Chavez ke shiga rana ta hudu na ci gaba da layi don yi wa gawar mamacin ban kwana; an kada gangar siyasa a kasar, inda zabe ke karatowa a cikin wata guda.

Jagoran adawa Henrique Capriles, ya amince zai nemi shugabancin ga 'yan adawa.

Mr Capriles zai kalubalanci Nicolas Maduro, wanda aka rantsar a matsayin Shugaban rikon kwarya awowi bayan da aka yi jana'izar Hugo Chavez.

A wata hira da manema labarai ta kafar Talabijin, Henrique Capriles ya zargi Nicolas Maduro da yin karya ga kasar kan batun lafiyar Mr Chavez.

Ya ce, Mr Maduro yana amfani ne da gawar chavez a matsayin wata madogara ga yakin neman zaben sa.

Hugo Chavez dai ya kada Mr Capriles a zaben watan Octobar bara.

A karon farko Mr Capriles ya yi nasarar hada kan 'yan adawar da kansu yake a rarrabe.

'Yan takara dai suna da damar yin rigistar shiga zaben har zuwa yau Litinin da yamma.

Za kuma a gudanar da zaben ne ranar goma sha hudu ga watan Aprilu.

Karin bayani