An cafke mutane 9 a Malawi bisa zargin juyin mulki

Malawi
Image caption Masu zanga zanga a Malawi

'Yan sanda a kasar Malawi sun kama mutane tara, ciki har da tsaffin ministoci takwas da kuma mai ci guda daya, bisa zargin yunkurin juyin mulki bayan mutuwar shugaban kasar Bingu wa Mutharika a bara.

Wani bincike da aka gudanar a hukumance ya gano cewa mutanen - wadanda suka hada da kanin Mr Mutharika, sun yi kokarin hana mataimakiyar Shugaban Kasa ta wancan lokaci Joice Banda, hawa kan karagar mulki.

An zarge su da baiwa sojoji umarnin su yi juyin mulki.

'Yan sanda sun harba hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa daruruwan masu zanga-zangar da suka taru a birnin Blantyre wadanda ke adawa da kama mutanen.