Ana shirya mana makirci- APC

A Najeriya, sabuwar jam'iyyar adawar nan da wasu jam'iyyu hudu suka dunkule da nufin kafa ta, wato APC ta ce ana shirya mata zagon kasa.

Jam'iyyar ta ce yunkurin da wasu ke yi na neman rajistar hukumar zabe ga wata jam'iyya mai suna irin nata, wato APC ko African People Congress da cewa makirci ne na bata mata tafiya.

Hukumar zaben Najeriya ta tabbatar da wannan yunkurin.

Dr Yakubu Lame jigo a jam'iyyar APC, ya shaidawa BBC cewa da ma sun san za a rina.

Dr Lame ya ce hakar masu yunkurin dai ba za ta cimma ruwa ba.

"A shirye muke kuma zamu yi duk abun da ya kamata domin ganin an yi mana rajista."

Ya ce; "tun da muka fito mu ke samun labarai iri-iri kan irin shirin da ake yi domin a bata mana tafiya."

"Akwai wadanda suka razana, shi yasa haka za su gani."