Bakin hayaki ya fito daga cocin Sistine

Saman Cocin Sistine
Image caption Saman Cocin Sistine

Manyan malaman cocin Katolika wato Cardinal-cardinal sun kada kuri'ar farko domin zaben sabon Paparoma.

Kuma kamar yadda aka yi tsammani, bakin hayaki ya fito daga saman cocin Sistine inda ake gudanar da zaben, abinda ke nuna cewa ba a kaiga zaben sabon Paparoman ba.

Za a kada kuri'a sau hudu a gobe Laraba da sauran ranakun da ke tafe har sai an kai ga zaben sabon Paparoman.

Tunda farko Cardinal-cardinal din sun yi addu'a kafin fara zaben sannan suka yi rantsuwar cewa za su boye sirrin yadda zaben ke gudana.

Karin bayani