Sudan ta Kudu za ta fara tura mai ta Sudan

Rumbunan ajiyar mai a Sudan ta Kudu
Image caption Kasashen na Sudan da Sudan ta Kudu ba sa ga maciji da juna

Jamhuriyar Sudan da Sudan ta Kudu sun amince da cigaba da aikin tura mai ta Sudan, bayan rashin jitu wa game kudaden da za a dinga biyan Sudan din.

Rashin jituwar dai shi ya kai ga Sudan ta Kudu ta dakatar da ayyukan hakar manta.

Sudan ta Kudu wacce ta samu 'yancin kanta daga Sudan a shekarar 2011, za ta koma hako mai a ranar 24 ga watan Maris da muke ciki.

An cimma hakan ne a wata yarjejeniya a Habasha.

Dukkanin kasashen dai sun dogara ne a kan mai, wanda Sudan ta Kudu ke hako wa, kuma a bi da shi ta bututan man da suka ratsa jamhuriyyar Sudan.

Haka kuma kasashen sun amince game da batun bakin iyaka.

Kuma za a kafa tudun muntsira, domin kara inganta batun tsaro a tsakaninsu.

Sannan zaman taron na Addis Ababa ya tattauna wasu yarjejeniyoyin cinikayya da wani kwamiti da zai yi aiki game da batun bakin iyakar.

A cewar wakilin BBC dake Nairobi, James Copnall batun alkawari game da cigaba da tura man ne zai fi daukar hankali.

Tattalin arzikin Sudan ta Kudu ya kasance a ruguje, tun bayan da ta tsaida hakar mai, abin da ya sa aka dakatar da ayyukan gina kasa, ita ma Sudan na jin jiki.

Idan aka mutunta wannan 'yajejeniyar, tattalin arzikin Sudan zai samu tagomashin dubban miliyoyin daloli daga kudaden da Sudan ta Kudu za ta dinga biya na fitar da man ta cikin Sudan.

Cikin kudaden har da wanda Sudan ta Kudu za ta biya, saboda kyale ta ta ci gashin kanta da Sudan ta yi, a cewar masu aiko da rahotanni.