An zabi sabon Paparoma

Image caption Farin hayaki shi ne ya tabbatar da zaben sabon Paparoman

Manyan limaman Roman Katolika sun zabi sabon Paparoma bayan da aka ga farin hayaki ya fito daga majami'ar Sistine da ke fadar Vatican.

Dandazon mutanen da suka taru a dandalin St Peter sun rude da ihu sannan kararrawa ta kada a lokacin da hayakin ya fito.

Ana sa ran bayyana sunan sabon Paparoman nan bada jima wa ba.

Shi ne zai maye gurbin Paparoma Benedict XVI, wanda ya yi murabus a watan da ya gabata yana mai cewa bashi da koshin lafiyar da zai iya ci gaba da jagorantar cocin.

Karin bayani