Rikici: Za'a tallafawa mata a Najeriya

Image caption Wasu mata da suka rasa 'yan uwansu a lokacin rikici

Saboda matsalar tsaro da ake fuskanta a wasu sassan Najeriya, gwamnatin kasar ta ce za ta taimakawa mata da suka rasa mazajensu a lokacin rikici ko kuma annoba.

Ministar kula da al'amuran mata a kasar, Hajiya Zainab Maina ta ce gwamnatin tarrayar kasar ta ware wasu kudade wanda aka baiwa gwamnotocin jihohin da ke fama da rikicin.

"mun fahimci cewa akwai matan da mazajensu suka mutu suka barsu da marayu kuma basu da abun yi.

"muna tanadin yadda zamu taimaka musu domi dogaro da kai." In ji Hajiya Zainab Maina.

Ministar har wa yau ta ce gwamnatin kasar taba duba yiwuwar tsaurara dokokin da su ka danganci fyade domin kare mata da kananan yara.

Ta ce matsalar fyade ta addabi duniya gabaki daya kuma dolene masu ruwa da tsaki su hada karfi da karfe domin magance matsalar.