'Yan mata na kamuwa da HIV a Afirka ta Kudu

Cutar HIV a Afirka ta Kudu
Image caption 'Yan mata na lalata da sa'annin iyayen su a Afirka ta Kudu

Ministan kiwon lafiya na Afirka ta Kudu yace kusan kashi talatin cikin dari na yara 'yan mata dake makaranta na dauke da kwayar cutar nan ta HIV, inda kashi hudu cikin dari na maza kuma ke dauke da kwayar cutar, kuma hakan a cewar ministan ya faru ne saboda yadda manyan mutane ke yin lalata da 'yan matan

Ministan yace a fili take cewa 'yan matan basa yin lalata tare da sa'annun su, amma suna yin hakanne tare da sa'annin iyayen su.

'Yan mata kusan dubu dari ne dai su ka dau ciki a shekarar 2011, kuma kusan dubu tamanin daga cikin su ne sun zubar da cikin a asibitoci da kuma dakunan shan magani

Karin bayani