Makwabtan Mali na cikin fargaba

Yayinda ake ci gaba da gwabza fada tsakanin 'yan tawaye da kuma dakarun da Faransa ke jagoranta a kusa da garin Gao na arewacin Mali, wani wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman a yankin Sahel Romano Prodi ya ce kasashe makwabtan Malin na cike da fargaba kan yadda mayakan 'yan kishin Islama ka iya tayar-da-kayar baya a kasashensu.

Furucin nasa ya zo ne a daidai lokacin da jakadan Amurka a Nijeriya ke cewa akwai rahotanin dake nuna cewa mayakan kungiyar nan da aka fi sani da Boko Haram na fita daga Nijeriyar suna nufa inda ake rikicin.

A watan Oktobar da ya gabata ne sakatare janar na majalisar dinkin duniya Banki Moon ya nada tsohon Piraministan na italiya kuma shugaban kungiyar tarayyar turai a matsayin jakada na musamman a yankin na Sahel.

Tun lokacin kuma ya gana gaba-da-gaba da shugabannin kasashen yankin.

Prodi ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa da Burkina faso da Nijar da Mauritania, sun nuna fargaba dangane da yaduwar rikicin.

A cewarsa, Kasar Chadi na da bambamci kadan da sauran kasashen, saboda tana da dakaru masu karfi.

A ranar 11 ga watan Janairun da ya gabata ne dai, Faransa ta kaddamar da hare-hare ta sama da kasa a yunkurinta na karya lagon masu tsattsauran ra'ayin addinin Islama wadanda suka kwace kashi biyu cikin uku na arewacin Mali.

Ko da yake harin da aka rinka kaiwa ba kakkautawa ya kai ga kwato akasarin wuraren da 'yan tawayen suka kwace kusan shekara guda ke nan, dakarun na Faransa da na Chadi suna fuskantar turjiya daga mayakan sa kan da suka buya a tsaunukan da ke kusa da kan iayka da Algeria.

Prodi ya ce,ya rage ga Kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya ya yanke shawara akan irin rawar da majalisar dinkin duniya za ta taka nan gaba a Mali.

Sai dai ya ce dole ne a samu wani tabbaci daga kasashen duniya cewa za a yi adalci wajen rarraba kudeden al'umma a arewacin Mali.

Shi ma da yake tsokaci, jakadan Amurka a Najeriya, Terrance Mcculley ya ce,masu kaifin tsattsauran ra'ayin addinin islama na ci gaba da komawa arewacin Mali duk da ayyukan da dakarun faransa ke yi a can.

Mcculley ya ce ya yi amanna,'yan Najeriya na jin cewa akwai alaka tsakanin masu tsautsauran ra'ayin addini a yankin Sahel da kuma masu tsattsauran ra'ayin addinin da ke ta da kayar baya a kasar su.

Sai dai kuma ya ki tattaunawa a kan shirye-shiryen Amurka na kafa sansanin jiragen da ba su da matuka a makwabciyar Najeriya wato Nijar, matakin da ke damun wasu a arewacin kasar inda musulmai suka fi yawa.

Karin bayani