Paparoma Francis ya fara aiki gadan-gadan

Paparoma Francis na daya
Image caption Paparoma Francis na daya

Paparoma Francis ya soma aikinsa na paparomanci tare da yin addu'o'i a Cocin Santa Maria dake Rome, kafin daga bisani ya gudanar da taron addu'o'i a Cocin Sisitine.

Daga baya kuma zai gudanar da taron addu'o'i a Cocin Sisitine.

Zai kuma soma shirin nada manyan jami'an da za su yi aiki tare da shi a fadar ta Vatican.

wannan ita ce wata damar da Paparoman zai yi amfani da ita wajen sauya wata majami'a dake cike da rikici.

Kuma zai nuna alkiblar da yake fatan majami'ar za ta dosa.

Shi ne mutumin Latin Amurka na farko da ya zamo Paparoma.

Paparoma Francis yana da shekaru 76 da haihuwa.

Dandazon mutanen da suka taru a dandalin St Peter sun rude da ihu sannan kararrawa ta kada a lokacin da hayakin ya fito.

Karin bayani