Wanene Paparoma Francis?

Pope Francis
Image caption Paparoma Francis ya nemi mabiya darikar Katolika su yi masa addu'a

An haifi Paparoma Francis na daya a kasar Argentina, kuma yana da shekaru 76 da haihuwa, shi ne Paparoma na farko da ya fito daga Latin Amurka.

A rayuwarsa ta aiki a Argentina, ya dukkufa ne wajen tabbatar da ganin an samu daidaito a al'umma da kuma ganin an kare hakkokin talakawa.

A kasar Argentina mabiya darikar ta katolika sun jinjinawa zaben na shi.

Mutane da dama dai ba su sanya shi cikin rukunin wadanda za'a iya zaba a matsayin Paparoma ba, amma a zaben da aka yi a baya da ya fito da Paparoma Benedict shi ne ya zama na biyu.

Ana dai girmama shi saboda illiminsa. Ya kuma yi karatun addini ne a Jamus kuma ya zauna a kasar Italiya.

Paparoma Francis zai kawo wani sabon salo ga shugabancinsa saboda shi ne Paparoma na farko dake darikar Jesuit ta Katolika.

Ya dai jagoranci al'ummar Katolika a Argentina a lokacin mulkin soji, lokacin da mutane da dama suke cikin ukuba a kasar, amma akwai wadanda suke sukarsa a wannan lokacin da cewa bai fito ya kalubalanci gwamnatin kasar ba.

Sabon Paparoman yana da ra'ayin mazan jiya ne, kuma yana adawa da lalata da auren jinsi daya da kuma zub da ciki.

Ganin irin gudunmuwar da ya bayar wajen ganin a samu daidaito a Argentina, ana ganin Cardinal Bergolgio zai ci gaba da ayyukan wanda ya gada ne na kokarin ganin ya hada kan al'ummar Katolika da kuma tabbatar da aldalci a duniya.

Amma ganin yadda wasu al'ummar Katolika ke juyawa cocin baya a wasu kasashen Turai, saboda matsalar lalata da kananan yara, sabon Paparoma Francis na farko na da babban Kalubale a gabansa.

Karin bayani