APC ta ce ba ja da baya a neman rajista

Buhari da Tinubu
Image caption Buhari da Tinubu

A Najeriya, manyan jam'iyyun adawar kasar da ke yunkurin hadewa su kafa jam'iyyar APC sun ce sun aike wa hukumar zaben kasar INEC da wasikar da a cikinta suke kira da ta kauce wa yin rajista ga wasu da ke neman rajista da irin sunan da suka zabar wa jam'iyyar su, wato APC.

Jam'iyyun sun bayyana hakan ne a wata sanarwa da suka gabatar wa manema labarai a Abuja ranar Alhamis.

Sanarwar tasu ta biyo bayan bayanan da aka samu ne cewa, wasu sun mika wa hukumar zaben ta INEC bukatar a yi musu rajista da sunan APC.

Tsohon gwamnan jihar Kano, Mallam Ibrahim Shekarau ya shaidawa BBC cewa yunkurin wadanda ya kira, " Yan zagon kasa" ba zai yi nasara ba.