Damuwa a kan iyakar Syria da Lebanon

Image caption Rikicin Syria nan nema ya shiga Lebanon sannu a hankali

Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya nuna damuwa game da irin hare-haren da ake kaiwa a kan iyakar Lebanon da Syria da kuma safarar makamai.

Kwamitin ya nuna fargabar cewa rikicin na Syria na shiga kasar Lebanon sannu a hankali.

Membobin kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya sun numa damuwa matuka akan irin tasirin da rikicin Syria yake a Lebanon.

Kwamitin yace hare-haren da ake kaiwa a kan iyakan kasashen biyu da kutse da kuma safarar makamai abun damuwa ne matuka.

Kwamitin ya bukace al'ummar Lebanon da kada su bari irin wannan na tashe-tashen hankalin da ake samu ya kaiwo tsaiko ga irin zaman lafiyar da aka samu a kasar.

Kwamitin dai ya yi kira ga sauran kasashen duniya da su guji abun da ka iya tsunduma Lebanon cikin rikicin na Syria.

Sanarwar ta kwamitin ya biyo bayan irin fargabar da ake na ganin cewa irin rarrabuwar kawunan da aka samu a kasar na iya faruwa a Lebanon.

Ana ganin irin wannan mataki da kwamitin ya dauka, matashiya ce ga kashen da ke goyon bayan Syria, musamman ma Iran, kuma ana ganin idan aka samu sauyi a gwamnatin Lebanon, zai yiwa gwamnatin Syria dadi.

Gwamnatocin kasashen yamma sunyi imanin cewa kungiyar Hizubullah da Iran ke goyon baya na ci gaba da taimakon gwamnatin gwamnatin shugaba Assad duk da kokarin da kasashen duniya keyi na gujewa hakan.

Jami'an diplomasiyya dai sun ce Iran na ci gaba da taimakawa gwamnatin Syria da makamai domin ta yaki yan tawaye.