Amurka ta soki gwamnatin Najeriya

Alamieyeseigha
Image caption Jama'a da dama sun soki matakin na yiwa Alamieyeseigha afuwa

Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya ce baiji dadin yadda gwamnatin kasar ta yi afuwa ga tsohon gwamnan jihar Bayelsa Diepreye Alamieyeseigha ba, wanda aka samu da laifin cin hanci da rashawa.

A sakon da ya fitar a shafinsa na Twitter, ofishin ya ce: "Muna kallon matakin a matsayin wani koma-baya ga yunkurin yaki da cin hanci da rashawa."

Hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati ta Najeriya EFCC ce ta kame Alamieyeseigha, kan zargin sace miliyoyin daloli lokacin da yake kan mukamin gwamnan jihar Bayelsa.

Daga bisani an tsige shi daga kan mukamin, sannan kotu ta daure shi bayan da ta tabbatar da laifin da aka tuhume shi da aikata wa.

Tsige shi daga kan mukamin ne ya bude hanyar daukakar shugaban kasa Goodluck Jonathan a siyasance - wanda shi ne mataimakinsa a wancan lokacin.

A makon nan ne gwamnatin Najeriya ta sanar da yin afuwa ga Alamieyeseigha da wasu mutane shida a kasar da suka hada tsohon dan takarar shugaban kasa marigayi Shehu Musa Ya'aradua da marigayi Janar Oladipo Diya.

Najeriya na daga cikin kasahen da ke kan gaba wurin sayar da man fetur ga kasar Amurka.

Karin bayani