Amurka na girke makaman kariyar makami mai linzami

Image caption Chuck Hagel ya yi nuni da yunkurin Amurka na kare kanta daga makami mai Linzami

Sakataren tsaron Amurka Chuck Hagel ya sanar da cewa Amurka za ta jingine kashin karshe na wani shirin samar da kariya daga makamai masu linzami na Tarayyar Turai.

Amurkar ta dauki anniyar samar da wata sabuwar garkuwa ta makamai masu linzami.

Kashin karshen na shirin kariyar daga makaman masu linzamin da aka shirya farawa nan da shekaru tara masu zuwa ya hada da tura na'urorin masu cafke makaman masu linzami a gabashin Turai.

Mr Hagel yace za a tura karin wasu na'urorin na cafke makaman masu linzami goma sha-hudu a Alaska tare da wata tashar radar ta hangen na'urori ko makamai a Japan don cimma abinda ya kira barazanar da ake kara samu daga Korea ta Arewa.

Shugaban kasar Korea ta Arewa Kim Jong Un ya yi barazanar mayar da babban birnin Amurka, Washington DC wajan musayar wuta.

Karin bayani