Pursunoni kusan dari biyu sun kubuta

Bayanai na ci gaba da fitowa game da wani hari da 'yan-bindiga suka kai kan wani gidan yari a garin Gwoza dake kan iyakar Nijeriya da Kamaru, cikin jihar Borno ta Nijeriyar.

Bayanai dai na cewa maharan sun kubutar da dukkan fursunoni kusan dari biyu dake tsare a gidan yarin, yayin da wani farar hula ya rasa ransa bayan da harsashi ya karkace ya same shi yayin da jami'an tsaron gidan yarin da 'yan bindigar ke musayar wuta.

Yan bindigar da ba san ko su wane ne ba sun zo a motoci da babura ne kuma har yanzu babu wani bayanin kama koda daya daga cikinsu ko kuma pursunonin da suka kubutar daga gidan yarin.