Najeriya da Amurka na musayar yawu

Image caption Najeriya da Amurka na musayar yawu kan afuwa ga Alamieyeseigha

Najeriya ta kira mataimakin Jakadan Amurka don nuna rashin amincewar ta da wata sanarwa ta hukuma da Amurkar ta bayar wadda ta soki lamirin afuwar da aka yi wa tsohon Gwamnan Jihar Bayelsa Diepreye Alamieyeseigha.

A wani sako da aka tura ta hanyar sadarwar nan ta Twitter a ranar Juma'a, wata babbar jami'a a ma'aikatar harkokin wajen kasar ta ce wannan afuwa za ta iya yin illa ga agajin da Amurkar za ta baiwa Najeriyar nan gaba.

Ma'aikatar harkokin wajen Najeriya ta bayyana kalaman na Amurka a matsayin shigar sharo ba shanu.

Sanarwar ta ce Shugaba Goodluck Jonathan ya yi amfani da karfin ikon da tsarin mulki ya ba shi na yi wa wasu afuwa.

Gwamnatin Najeriyar dai ta yiwa wasu yan kasar afuwa a wannan makon ciki har da Toshon gwamnan Jihar Bayelsa Diepreye Alamieyeseigha wanda aka tsigeshi daga kan karagar mulkin Jihar daga bisani kuma aka kama shi da laifin cin hanci a kasar.

Masu bincike dai sun ce tsohon gwamnan yayi amfani da kudaden gwamnati ya mallaki gidaje a Birtaniya da kuma Najeriya da suka kai sama da dala miliyan goma.

Karin bayani