Gwamnatin Pakistan ta kafa tarihi

Raja Pervez Ashraf
Image caption Gwamnatin Pakistan ta kammala wa'adin ta

Gwamnatin Pakistan ta kafa tarihi a matsayin zababbiyar gwamnati ta farko tun lokacin da aka kirkiri kasar, wacce ta kammala cikakken wa'adinta na shekaru biyar

An dai rushe majalisar dokoki an kuma nada wasu masu gudanar da mulki na riko da zasu gudanar da harkokin gwamnati har lokacin da za a gudanar da zabubuka cikin kwanaki casa'in

Ana tsamanin Prime Minista Raja Pervez Ashraf zai zauna a ofis har zuwa lokacin da za aamince da wanda zai maye gurbinsa na rikon kwarya

Masu aiko da rahotanni sunce ana kallon kammala wa'din gwamnatin a matsayin babban cigaba, amma Pakistan har yanzu na fuskantar tabarbarewar harkokin tsaro da kuma kalubalen tattalin arziki

Karin bayani