Paparoma na son Coci ya tallafawa Talaka

Sabon  Paparoma Francis
Image caption Paparoma ya ce yana son yiwa talakawa aiki

Sabon Paparoma Francis ya gana da manema labarai a birnin Rome, kuma ya bayyana cewa dole ne majami'ar Catholican ta tuna cewa burin ta shine na yiwa talakawa aiki

A jawabin sabon Paparoman ga daruruwan 'yan jarida , ya bayyana cewa ya zabi ya kira kansa ne da sabon sunan sa domin ya ci gajiyar sunan St Francis na Assisi

Wannan ita ce ganawarsa ta farko da 'yan jarida tun bayan da aka zabe shi a matsayin paparoma ranar larabar da ta gabata.

A karshe Paparoma Francis ya kuma yi kira ga jama;a da su maida hankali ne ga Yesu Almasihu ba wai shi kansa ba.

Karin bayani