Ana zaben rabagardama a Zimbabwe

Image caption Mugabe da Tsvangirai sun yi kira da magoya bayan su, su yi zaben rabagardama

A yau, Asabar 'yan kasar Zimbabwe sun fara kada kuri'unsu a wani zaben raba gardama game da sabon kundin tsarin mulkin kasar wanda zai share fagen gyare-gyaren demokradiyyar kasar.

Jam'iyyar Shugaba Mugabe Zanu-PF da ta tsohon jagoran 'yan adawa MDC watau Prime Minista Morgan Changarai duk sun goyi bayan sabon shirin.

Tsarin mulkin ya kawo shawarar sauye sauye kan wa'adin mulki na tsawon shekaru biyar - sau biyu ga Shugaban kasa.

Haka kuma ya yi tsokaci kan wata ayar doka dake bayar da kariya ga 'yancin bayyana ra'ayi ga 'yan kasar.

Masu aiko da labarai sun ce kamfe da aka rinka yi na zaben raba gardamar ya tayar da kaimin siyasa gabanin zaben Shugaban kasar da za a yi nan gaba a bana a kasar ta Zimbabwe.

Karin bayani